ABNA24 : Majiyar muryar JMI ya nakalto Ali Asgar Munison da kuma Felix Plasencia suna fadar haka a jiya Laraba a wani taron yan jarida da suka kira a nan Tehran.
Munison ya ce ma’aikatarsa ta taimakawa ‘yan kasuwa masu zaman kansu a kasar Iran gina Otel Otel har guda 498. Sannan a shekara ta 2019 da ta gabata kasar Iran ce kasa ta biyu a duniya wajen saurin fadada bangaren yawon shakatawa a duniya.
A nashi bangaren Felix Plasencia ya ce Tehran da Caracas zasu yi musayar kwarewa a bangaren yawon shakatawa a tsakanin don samar da ci gaba a wannan fagen a kasashen biyu.
342/